15 Afirilu 2021 - 14:19
NATO Za Ta Janye Dakarunta Daga Afganistan Kafin Ranar 1 Ga Watan Mayu

Kasashen kawaye na kungiyar tsaro ta NATO, sun kudiri anniyar janye tagwar dakarunsu a kasar Afganistan, kafin nan da ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.

ABNA24 : A wata sanarwa da kungiyar ta NATO, ta fitar, ta ce za’a aiwatar da shirin wanda ya hada da janyewar dakarun daga Afganistan cikin tsari.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Joe Biden, ya shaida cewa Amurka zata janye sojojinta daga Afganistan kafin nan da zuwa ranar 11 ga watan Satumba.

A lokacin da ya ke sanar da hakan jiya, shugaba Biden, ya bukaci ‘yan Taliban da su cika alkawarin da suka dauka, na ba zasu yi barazana ga Amurka ba.

A cikin jawabin nasa daga fadar white House, Biden ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen wannan yakin da baida karshe.

Amurka dai ta kwashe shekara ashirin tana yaki a Afganistan tun bayan harin 11 ga watan Satumban 2001, kuma Joe Biden shi ne wani shugaban Amurkar na 4 da zai jagoranci ayyukan sojojin a Afganistan, ya kuma yi alkawarin cewa ba zai mika wannan aikin ba ga wani shugaba na biyar ba.

Ya kuma ce duk tsarin janye sojojin na Amurka zai fara a ranar 1 ga watan Mayu, amma ba za’a aiwatar da hakan ba cikin gaggawa.

342/